Buhari zai kammala wasu aiyuka a zangon mulkinsa na biyu -Sanata Gaya


Shugaban kasa Muhammad Buhari zai kammala wasu aiyuka a zangon mulkinsa na biyu, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, mai wakiltar mazabar Kano Ta Kudu, shine ya bayyana haka a fadar shugaban ƙasa.

Gaya bayyana haka lokacin da yake magana da yan jarida masu dauko rahoto daga fadar shugaban kasa.

“Game da aiyukan titi ya kamata mu godewa shugaban kasa Buhari kan ƙoƙarin da yake yi. Allah ya kara masa lafiya da karfin jiki ya cigaba da yi. Na sani cewa zai kaddamar da wasu aiyukan a shekarar 2018 kuma wadanda ba a kammala ba za a kammala su a zangon mulkinsa na biyu,”yace.

“Munyi farin ciki sosai da ya bada kwangilar aikin hanyar Kano zuwa Abuja da  za a kashe biliyan ₦165.Kuma kasancewa ta shugaban kwamitin aiyuka babu wata gwamnati cikin shekaru  16 da ta zuba kuɗi sosai a aikin titi kamar wannan gwamnati.

“Kasafin kudin 2011-2014 biliyan ₦24 kawai aka warewa bangaren aiyuka amma a shekarar 2016 lokacin da Buhari ya hau mulki  muna da kasafin kudin ɓangaren aiyuka da yakai biliyan ₦200 a shekarar 2017 muna da biliyan ₦400 yayin da a shekarar da 2018 muke da kusan biliyan ₦500.

“Muna gyara titunanmu waɗanda kuma akayi watsi da su shekara da shekaru yanzu yan kwagila sun koma bakin aiyukansu.”


Like it? Share with your friends!

0

You may also like