A yau Talata ne shugaban kasa Muhammad Buhari zai koma birnin Landan domin likitoci su duba lafiyarsa.
Mataimakin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da yafitar.
Shehu yace ana sa ran tafiyar za ta dauki tsawon kwanaki hudu.
A cewar Shehu likitan Buhari shine ya nemi shugaban ya dawo a duba lafiyarsa bayan da suka hadu lokacin da jirgin shugaban kasa ya ya da zango a birnin London akan hanyarsa ta dawowa gida Najeriya bayan ziyarar aiki da yakai kasar Amurka.
Shehu ya ce da zarar shugaban kasar ya dawo zai kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu ya zuwa jihar Jigawa.
A shekarar 2017 shugaban kasar ya shafe kwanaki 150 a birnin London yana jiyar wata cuta da har yanzu ba a bayyana ba.