Shugaban kasa Muhammad Buhari zai shafe kwanaki 4 a birnin London, Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasar ya shaidawa BBC.
Buhari ya koma birnin London a ranar Alhamis bayan halartar babban taron majalisar dinkin duniya da ya gudana a birnin New York “zai kasance a birnin London har zuwa ranar Litinin mai zuwa,” ya shaidawa BBC Hausa.
Babu dai wani karin bayani da aka bayar kan dalilin ziyarar shugaban zuwa birnin na London a wannan lokacin ,amma tun da fari Adesina ya bayyana cewa shugaban zai tsaya a birnin London akan hanyarsa ta dawowa gida Najeriya.
A wannan shekarar kadai Buhari ya shafe kwanaki 153 yana jinya a birnin London.
Har yanzu dai fadar shugaban kasa taki bayyana cikakken ciwon dake damun shugaban,duk da irin kiraye-kirayen da jam’iyun adawa sukayi na a bayyanawa yan Najeriya cikakken abinda yake damun jagoransu.