Buhari zai tafi ƙasar Faransa ranar Litinin


Shugaban ƙasa Muhammad Buhari a ranar Litinin zai tashi daga Abuja zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa domin halartar wani taro.

A wata sanarwa da Femi Adesina mai magana da yawun shugaban kasar, yafitar a ranar Lahadi yace Shugabannin kasashen duniya sama da hamsin ne zasu halarci taron.

Ya ce shugaban na Najeriya zai samu rakiyar gwamnonin jihohin Kano, Adamawa da kuma Ondo tare da ministan harkokin waje da na muhalli.

 “Taron na haɗin gwiwa tsakanin Majalisar Dinkin Duniya, Bankin Duniya da kuma gwamnatin Faransa da kuma wasu kungiyoyi da bana gwamnati ba zai mayar da hankali kan maganin illar da sauyin yanayi ke kawowa,” sanarwar tace.

You may also like