Shugaban Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta goyi bayan sauya sauye a kundin tsarin mulkin kasa wanda zai ‘yanta kananan hukumomi daga dabaibayin gwamnatocin jahohi ta yadda za’a inganta rayuwar talaka.
Ya fadi haka ne yayin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar kananan hukumomin Nijeriya a jiya Alhamis a Abuja inda ya ce ana bukatar sauyae sauye a kundin tsarin mulkin kasa da gaggawa domin a kayyade irin mu’amalar da ke tsakanin matakan gwamnati guda uku.
Ya kira rashin jituwar da ke tsakanin gwamnatocin jaha da gwamnatocin kanana hukumomi mummunan matsala ga tsarin mulkin kasa.