Buhun Taki Zai Koma Naira 5500


Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da biyan naira biliyan 22 ga dillalan amfanin gona, dan tabbatar da taki ya koma rabin kudinsa a yanzu dai taki mai nauyin kilo 50 yakan kai fiye da naira dubu 10.

A farkon shekarar nan ne ministan noma da raya karkara Chief Audi Ogbeh, ya sanarda  cewa gwamnatin tarayya zata bada tallafin kashi 50 akan farashin taki.

Yayinda a baya manoma na Sayan takin akan farashin naira dubu 10, harzuwa naira dubu 20.

You may also like