An Bukaci Najeriya Ta Rufe Makarantun Turkiyya a Kasar


 

 

 

 

Gwamnatin Turkiyya ta bukaci Najeriya ta rufe makarantun nan na kudi na ‘yan kasar Turkiyyar da aka fi sani da Nigerian-Turkish International Schools.

Makarantun dai na ‘yan Turkiyya sun yi matukar karbuwa wajen ‘yan Najeriya musamman masu hannu da shuni. Inda suke ta rububin kai ‘ya’yansu ba ji ba gani don ganin sun sami ilimi ingantacce.

Musamman a yanayin da ake ta ci gaba da samun tabarbarewar ilmi a kasar tsawon shekaru. To gwamnayin Turkiyya dai ita ce ta nemi da a rufe makarantun biyo bayan harin juyin mulkin da sojoji suka kai.

Wanda suka yi kokarin hambarar da gwamnatin su Racep Tayyip Erdogan, wanda bayan gazawar juyin mulkin ne gwamnatin ke ta faman kai samame tare da kame dubban jami’an soji da na shari’a a kasar.

Cikin zargin kitsa juyin mulkin har da wani malami mai gudun hijira a nan Amurka da ake kira Fethullah Gulen, wanda kuma shine attajirin da ke da wata kungiyar mabiya ta Gulen Movement da su ke da wadannan makarantu.

You may also like