‘Bunkasa Aikin Noma Zai Kawar Da Talauci A Nijeriya’


 

 

Fitaccen manomin nan, kuma Shugaban jam’iyyar(NDP) reshen jihar Bauchi, Malam Abubakar Dan Dada ya bayyana cewa matukar gwamnatocin jihohin kasar nan suka ba da fifiko wajen bunkasa aikin noma da kiwo, to za a yi bankwana da talauci a kasar nan baki daya. “Idan aka yi haka, tabbas cikin kankanin lokaci Nijeriya za ta samu bunkasar tattalin arziki. Duk kasar da ba ta iya ciyar da kanta, ba ta daga cikin kasashen da suka ci gaba a duniya,” in ji shi.

Malam dan Dada ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke Unguwar Bakin Kura a kwanakin baya.

Ya ci gaba da cewa, “saboda haka muna ba da shawara ga matasa da sauran masu ruwa da tsaki a tsakanin al’umma su fahimci cewa akwai alhairi sosai a harkar noma da kiwo, kuma ina goyon bayan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na tilasta wa ‘yan kasa cin shinkafar da aka shuka na gida.”

Manomin ya ci gaba da bayyana cewa, “a matsayina na Tsohon manomi, duk inda mutum ya je a bana zai ga mutane da dama sun yi noma sakamakon yadda abinci ya yi tsada a kasuwannin kasar nan. Nijeriya na daya daga cikin kasashen da suke da dukiya, amma babbar matsalar da ake fuskanta, mafi yawan al’umma zuciyarsu ta mutu, kowa so yake yi a ba shi yana zaune.”

Daga nan sai ya bayyana cewa, babu wata al’umma da za ta samu ci gaba mai amfani ba tare da matasa ba, don haka ya zamo wajibi kowa ya kama sana’a, sannan kuma a hada da neman ilimin addini da na zamani.

“Daga karshe muna fata Gwamnonin kasar nan da Shugaba Muhammadu Buhar,i bayan an bunkasa aikin noma da kiwo, ya kamata a farfado mana da masana’antun da suka kwanta dama, musamman a shiyyar Arewa maso Gabas, da ma Nijeriya baki daya,” in ji shi.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like