Iran za ta bunkasa alakarta da kasashen nahiyar Afirka
Shugaban kasar Iran, Dr. Hassan Rauhani ya ce; Bunkasa alaka da kasashen nahiyar Afirka yana daga cikin siyasar jamhuriyar musulunci ta Iran.
A yayin ganawar da shugaban kasar ta Iran ya yi da ministan harkokin wajen kasar Cote De Voire, Abdullah Mabry a yau litinin anan birnin Tehran, ya ce; Iran a shirye ta ke, ta bunkasa alakarta da kasar Cote De Voire ta kowace fuska, musamman ma dai a fagen tattalin arziki.
Rauhani ya kara da cewa; Kasashen biyu suna da damar da za su yi aiki tare da kuma bunkasa alaka.
Har ila yau, shugaba Rauhani ya yi ishara da ci gaban da Iran din ta ke da shi, a fagagen wutar lantarki da gida madatsun ruwa da hanyoyi da za ta iya taimakawa kasar ta Cote De Voire.