BURIN ZUCIYA: Kalamai 25 Da Mata Ke Yi, Wadanda Maza Ba Sa Fahimta


 

Ina yi wa membobin Majalisar Burin Zuciya da dukkanin masu karatun jaridar Leadership Hausa fatan alheri da fatan samun babban rabo a wannan babban rana ta Jumma’ah. Allah Ya sa yadda muka ga farkonta lafiya, Ya sa mu ga karshenta lafiya, sannan ya kara sada mu da dukkan alheran da ke cikinta, Ya kuma kare mu daga dukkan sharrin boye da na bayyane, amin.

Na ci karo da wannan makalar a cikin wasu bincike-binciken da nake gudanarwa kan halayen mata, shi ne na ga yana da kyau membobinmu a wannan majalisa, musamman maza su fahimci wasu daga cikin halayen. Daga bisani, mu tattaro ra’ayoyin sauran jama’a, makaranta wannan jarida mai farin jini.

A binciken nawa, na fahimci babbar matsalar da maza ke fuskanta a kan zama da mata a yau shi ne rashin fahimtar yarensu. Ma’ana Lugga ko salon da zantukansu da inda maganarsu ke fuskanta. Amma kafin nan, ba ri mu yi tsakaci kan mace da yadda take gudanar da harkokinta a zahirance.

Masana harkokin mata, sun tafi a kan cewa mace ta fi aiki da zuciya fiye da kwakwalwa, sabanin namiji da ke aiki da tsantsar kwakwalwarsa, gami da hikimar da Allah Ya huwace masa. Bisa wannan dalilin ne idan mutum ya aikata wani abu, a ce da shi, ‘Haba wane…! Me ya sa kake abu kamar mace?’ Nesa ba kusa ba, namiji ya dara mace zurfin tunani da nazari bisa wannan dalilin. Hakan kuwa ya samo tushe ne daga cikin littafin Allah mai tsarki, wato Alkur’ani; inda Allah (SWT) da kanSa Ya zayyano martabobin namiji fiye da mace, sannan bayyana dalla-dalla fifikon namijin bisa mace, kamar yadda malamai suka karantar da mu.

Amma ina son masu karatu su gane cewa, zan takaita wannan tattaunawar  a kan matanmu na wannan zamanin. Domin kada wani ya tashi da husumarsa ya ce, ina kokarin muzanta mata a Musulunci.

Sanin kanmu ne cewa akwai manyan bayin Allah (mata), wadanda Allah Ya zaba a cikin addinin Musulunci, wadanda kuma suka taka muhimmiyar rawar ganin Musulunci ya tabbata. Su zababbu ne na Allah, su iyaye ne abin alfahari gare mu, sun kasance fitilu a gare mu. To, wannan makalar tana kallon rayuwarmu matanmu ne na yanzu. Da fatan an fahimta.

Me ya sa aurarrakinmu na zamanin nan ba sa yin karko? Me kuma ya sa maza suka kasa fahimtar abokan zamansu? Bisa wani dalili ya sa mata ba su da kunyar kallon namiji, sannan za su iya furta masa kowace irin kalma da ta zo bakinsu! Ina alkunyar da aka fi sanin mace da ita? Me ya sa aka watsar da kyawawan al’adu, wadanda suke zame wa mutane abin koyi?

Kafin mu amsa wadannan tambayoyin, yana da kyau mu kalli wasu zantukan da na binciko, a wani nazarin musamman da na gudanar da halayen mata kamar yadda na fadi a sama, ko maza za su iya daukar darasi a kai? Ga su nan kamar haka:

 

 1. ‘Na Amince’ – Saboda irin shu’umci na mace, a mafi yawan lokuta, ba haka abin yake ba, ka zama mai lissafi da basira wajen karbar wannan kalma.

 

 1. ‘Na Gode’ – Kalmar na gode ita ce akwai matsala, ko kuma da sauran rina a kaba!

 

 1. ‘Ci Gaba’ – Wannan wani umarni ne na je-ka-ka-gani! Idan kana son zaman lafiya, kada ka yi hakan!

 

 1. ‘Ba Komai’ – Idan mace ta kalli tsabar idanunka ta ce maka ‘ba komai,’ ka sani cewa akwai babbar magana a kasa, sai ka gaggauta neman mafita.

 

 1. ‘Shin Kayan Nan Sun Bayyana Kiba Ta?’–Fassarar wannan kalma ita ce, ‘Shin ni mummuna ce?’ Amsarka kada ta wuce: ‘A’a’!!!

 

 1. ‘Watakila’ – Idan mace ta yi amfani da wannan kalmar, kada ka bata wa kanka lokaci, tana nufin abin ba zai yiwu ba kawai!

 

 1. ‘Da Dai A Ce…’ – Wannan ma wata kalma ce da mata ke amfani da ita, mai harshen damo mai nufin ba a yarda da kai ba. Don haka, kada ka bata wa kanka lokacin bayanin wai dole sai ta yarda da kai!

 

 1. ‘Ya Yi Daidai’ – Kana jin wannan kalma daga bakin mace, kawai ka dauki na Annabawa – wato hakuri! Ba za ta kara dawowa kanka ba!

 

 1. ‘Komai Ya Wuce’ – Tabdijan! Kana jin haka, to ka fara azumi da neman tsari daga abubuwan da za su biyo baya. Galibi wannan kalma ce da suke nufi, ‘Bari zan yi tunanin matakin da zan dauka a kanka’.

 

 1. ‘Kana Ji Na Da Kyau?’ – Malam kada ka yarda mace ta samu galabar fada maka wannan kalmar, don haka, ka rika karantar lokutan da za ka rika ba ta umarni. Idan ka kuskura ka hau nuna mata kai ne namiji, ka fi ta matsayi, a daidai lokacin ne idanunta za su rufe, ta nuna maka cewa ba ta damu ba. Kuma ba za ta kara bin umarninka ba!

 

 1. ‘Zabi Na Gare Ka’ – Idan kana tsamanin ta ba ka zabi ne ka yi abin da kake so, to ka yi babban kuskure. Tana nufin, ‘Ka gama tsalle-tsallenka, amma ni na san gaskiyar abin da ya faru, kuma zan yi zabin abin da zan aikata.’ Saboda haka, duk sanda za ka fadi hukunci, kada ka kuskura ka bayyana mata dukkanin matakan da kake shirin dauka idan abin da kake tsammani bai tabbata ba.
 2. ‘Dariya Da Shewa’ – Idan mace ta yi dariya har da shewa a gabanka, matukar ka fara jin dadi – hakika sunanka sakarai! Galibi abin da ke zuciyarta shi ne, ‘Ban zaci zan iya ci gaba da tsayawa gabanka ina sauraren sakarci da wauta ba!’

 

 1. ‘Minti Biyar’ – Idan mace ta ce maka minti biyar. Kawai ka yi alwala ki tafi masallaci, bayan ka dawo ka nemi waje ka kwanta ka ci gaba da kallon talbijin ko ka gudanar da wasu al’amuranka, domin tana nufin awa daya ne!

 

 1. ‘Duk Abin Da Ka Fadi Daidai Ne!’ – Wannan babbar kalma ce da ke nunin cewa akwai matsala kwance a kasa. Matukar ka yi kuskuren daukar mataki cikin hikima da basira, sunanka ‘Sorry’!

 

 1. ‘Na Gode Matuka’ – Wannan ya sha bamban da kalmar da muka fadi a lamba ta biyu a sama. A nan tana nufin har zuci, tana miko godiya.

 

 1. ‘Godiya Mai Tarin Yawa’ – Wannan kalma kuma ta bambanta da duka sauran. Ida ta fadi maka haka, kada ka kuskura ka fara jin dadi, domin matsala ce a gaba. Idan ka yi kuskure, za ta mayar da kai lambata da 12, wato ‘Sakarai!’ Sai dai ka bi ta hankali, har ka gano bakin zaren.

 

 1. ‘Kada Ka Damu Da Wannan…’ – Lallai wannan kalma babba ce, domin akwai alamun ta yi maka kashedi a baya cewa, ba ta son abu kaza, ko kuma tana son ka yi mata wani abu, sannan ka amsa cewa za ka yi.

Daga bisani, aka samu akasi, idan ta ce maka ‘kada ka damu’ ka sani cewa ta yi maka hukunci ne da lamba 14 da muka ambata a sama!

 

 1. ‘Mu Je Duk Kantin Da Kake So’ – Idan matarka ta fada maka haka, ka sani cewa tana son ka kai ta wurin da take so ne. Idan ka dauke zuwa wajen daban, to ka saurari abin da ka-iya tasowa!

 

 1. ‘Ina Da Magana Da Kai’ – Abokina, ka mutu kawai!

 

 1. ‘Me Kake Yi Haka?’ – Wannan kalma na nuni da cewa kana yin abin da ba ta so ne. Sai ka auna yin sa da barinsa, wanne ya fi mahimmanci a zamanku, sannan ka yi hukunci a kai.

 

 1. ‘Me Ya Sa Kake Son Ka Aikata Wannan Abin?’ – Tambaya ce kuma ba tambaya ba! Tana nufin ka dakata da wannan abin da kake aikata a yanzu, ka sake wani nazarin!

 

 1. ‘Ya Kamata Ka Rika Fahimtar Magana!’ – Tana nufin ka rika jin shawarwarinta. Kuma ka rika girmama zantukanta.

 

 1. ‘Ban Yi Fushi Ba’ – Tana matukar fushi da kai. Idan ba rami, me ya kawo labarinsa!?

 

 1. ‘Wannan Abin Zai Maka Kyau…’ – A duk sanda ka ji mace ta nuna maka abu cewa ya kamata ka mallake shi, hakika ita ce mai son abin! Tana nufin ina son wannan abin!!

 

 1. ‘Ba Na Son Na Kara Yin Wannan Zancen’ – Idan mace ta fadi haka, tana son ka matsa a wajen, ba ta kaunar ganinka. Kwakwalwarta a lokacin neman tattara bayanai ne masu hadari a kan ka!

 

Wadannan su ne kadan daga cikin zantukan mata da na ci karo da su a yayin da nake gudanar da binciken musamman game da halayensu, kamar yadda na fadi a baya. har ila yau, idan an lura dukkan zantukan sun tafi a sabanin hakikaninsu. Hakan ya kara tabbatar min da wani Hadisi da na karanta, wanda aka samo daga daya daga cikin jikokin Manzo Muhammad (SAW), wato Imam Muhammad Al-Bakir (as), da ya fada cewa, “Idan ka shawarci mace a kan abu, duk maganar da ta fada maka, ka zabi akasin zancen, domin gaskiyarsu a koda yaushe, yana daidai da sabanin abin da suka bayyana.”

Ina fata Membobin wannan Majalisa ta Burin Zuciya, da masu karatun jaridar Leadership Hausa baki daya, za su tattauna, su aiko da na su ra’ayin.

Sai na ji daga gare. Na ku har kullum;

 

Abban Umma (Madugun Majalisar Burin Zuciya) (B/014/K/KAD). 08033225331.

Sakonnin Membobi Da Masu Karatu

 • Da Tashin Hankali Da Tashin Shinkafa, Wanne Ya Fi?

Assalamu alaikum Abban Umma, ina son ka tambaya min jama’a don Allah, wai shin da tashin hankali da tashin shinkafa wanne ya fi? Ma’ana da tashin boma-bomai da tashin masarufi, wane ya fi tashin hankali a yau? Mu zamto masa zaton alheri da tunani ga shugaban kasa, mu tsaya da du’a’i komai maganinsa Allah.

Daga Muzammil (Muzjam), Turakin New Nigerian. 08060907930.

 

 • Ina Taya Hajiya Shafa’atu Murna

Salam Hajiya Shafa’atu, muna miki Addu’ar Allah Ya ba ki ikon rike shugabanci mai cike da gaskiya da amana da hakuri. Kuma ina daida da Abban Umma.

Sako Daga Grema Mah’d Isa, Damaturu. 08034575067.

 

 • Kira Ga Gwamna Ganduje

Salam edita don Allah, ka mika mini sakon gaisuwa ta zuwa zababben gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje. Tanga mai tsawon zamani, Khadimul-Islam. Muna rokonsa da ya taimaka ya yi mana hanya daga Badume zuwa Tsaure.

Daga Mustapha Yunusa Tsaure, Bichi, Jihar Kano (Mawakin Mama Hafsa Gwaggo). 08093201093.

 

 • Na Samo Masoyiya Mai Mutunci

Assalamu alaikum, gaisuwa ga Abban Umma tare da fatan alheri ga masoyanka da mu na duniya baki daya. Don Allah ina son masoya su taya ni da addu’a, Allah ya ba ni masoyiya mai sona tsakani da Allah ba don kudi ko wani sha’awar abin duniya ba. Mace wadda take saliha, mai fara’a, iya magana, mutunci, karamci, wadda ba hantsi leka-gidan-kowa ba ce, don gudun yaudara. Don kullum addu’ata, kada na yaudari masoyiyata, hakan ni ma ba na son hakan tun lokacin da na yi rashin tsohuwar masoyiyata. Na gode.

Daga Shamsuddeen, 08103445212.

 

 • Majalisar Neja Ta Nada Sabon Mataimaki…

Salam, ina mai sanar da ku cewa Majilisar reshen Neja ta mince Malam Nura Aliyu Makwa ya zama Matimakin Shugaba na biyu, wanda duk zaman da za a yi a Makwa, ya zama jagoran taron.

Daga Bello Dandin Mahe (Shugaba na Jihar Neja) (B/039/Z/NEJ). 08034275846

 

 • Batun Zabe: Kira Ga Shugabannin Jihohi

Assalamu alaikum Abban Umma, yau na shigo ne don in bawa takwarorina Shugabanni jihohi shawara dangane da zabe mai zuwa, don ALLAH a matsayinmu na Shugabanni, kar fa mu manta mune iyayen Majalisa a jihohi saboda haka ina hore mu da mu tabbatar da adalci a jihohi gama dukkanni ‘yan takaran namu ne, wato muna uwa daya uba daya a Majalisar, mu yi hattara ga abin da ya gudana a wasu kungiyoyi makwabta.

Har ila yau kuma, ina jinjinawa hukumar zabe, karkashin jagorancin Kwamared Auwal Kontagora, bisa kokarinta na tabbatar da zabe cikin tsanake.

Bayan haka muna baran addu’o’in daga gare ku saboda mahaifiyar PRO namu wato Malam Aminu, kuma wakili a hukumar zabe  bata da lafiya sossai a asibiti tun kwanaki. Saboda haka ga mai son yi masa jaje a tuntube shi ta wannan lambar: 08093214003.

Naku Hassan Kaku-Zee, Shugaban Majalisar Burin Zuciya, reshen Jihar Borno (B/227/Z/ MAID). 07084556000.

 • Martani Ga Maryam Suleja

Assalamu alaikum Abban Umma – Sarkin soyayya! Ina yi maka fatan alkairi da fatan an yi Sallah lafiya. Na ji Maryam Suleja tana wata magana cewa wai namiji ba dan goyo ba ne, haba Maryam! Me yai zafi haka, har kike furta wannan maganar?

Don Allah Maryam a yi soyayya saffa-saffa, a wannan lokacin ‘yan mata sun fi maza yaudara ko dai  kin yaudari wani saurayin ne, ki ka juya maganar har da cewa ‘yan mata su yi hattara? Ni kuma ina kira ga samari da mu yi hattara da ‘yan matan zamani sun yi fice wajen yaudarar samari za ka samu wata sai an sa mata rana ma da wanda ya dade yana sonta, amman lokaci daya, za ta nuna masa cewa fa na sake saurayi ta hango mai hannu da shuni don Allah Maryam ki duba wannan maganar idan ana batun yaudara, ai sai ‘yan mata!

Daga Abdullah Muhammad Inuwa, Kabo, Kantsauni. 08067880649.

 

 • Godiya Ga Shugaba Buhari

Edita mai albarka, don girman Allah, ka ba ni fili in nuna godiyata ga Shugaba Buhari bisa ga nadin da ya yi wa Matashiya Hadiza Bala Usman na Shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa. Nadin ya kara nuna gwamnati na tafiya da matasa. Muna yi mata fatan alheri, muna ba ta shawara da ta kara sanya kishin kasa a zuciya kuma ta kawo sabbin dabarun da za su taimaki gwamnati kara inganta tattalin arzikin kasar nan. Daga Amiru Isah Bakori 07068147933.

 • Taron Membobin Katsina

Salamu alaikum.majalisar jihar Katsina na farin cikin sanar ma daukacin membobinta cewa za a gudanar da taro a ranar Talata mai zuwa in Allah ya kai mu.

Za a gudanar da taron ne a Makarantar Firamare ta Filin Samji dake cikin garin Katsina. Allah ya bada ikon halarta, ameen.

Sanarwa Sakataren Watsa Labarai. 08130000700

 

 • Batun Tantance Ma’aikatan Katsina…

Salam, ina son ka ba ni dama in yi kira ga ma’aikatan Jihar Katsina game da tantance ma’aikata da ake yi da su yi hakuri. Allah ya ba mu nasara, amin.w

Daga Saminu Mayentea Batsari. 08166016029.

You may also like