Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa babban burinsa da ya sa gaba shi ne na zama mutumin da ya fi kowa tallafawa marasa galihu a nahiyar Afrika.
Attajirin wanda a halin yanzu shi ne ya fi kowa arziki a Afrika ya ce, zai ci gaba da amfani da dukiyarsa da muryarsa wajen taimakawa na samun ci gaba a Nijeriya da Afrika baki daya.