Burtaniya Ta Dawo Da Yan Najeriya 35 Gida


Gwamnatin Burtaniya ta dawo da wasu yan Najeriya 35 zuwa gida bayan da ta same su da aikata laifukan da suka saba dokokin shige da fice na kasar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya rawaito cewa mutanen da aka koro daga Burtaniyar sun sauka a filin jiragen sama na Murtala Muhammad dake Legas.

Mutanen da suka hada da 30 maza da kuma mata 5 an dawo dasu gida ne cikin wani karamin jirgi da akayi shata. 

Mai magana da yawun rundunar yan sanda dake filin jirgin saman DSP Joseph Alabi, ya tabbatar wa da NAN faruwar lamarin. 

Mutanen sun samu tarba daga jami’an hukumar kula da shige da fice ta kasa da kuma na hukumar yaki da fataucin mutane ta kasa NAPTIP. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like