Burutai Ya Rabawa Sojoji Baburan Yaki Domin Fadan Karshe da BokoHaram 



Dakarun sojojin sun sha alwashin fatattakar ‘yan Boko Haram tare da gamawa da su daga mabuyansu dake dajin Sambisa a karo na karshe nan bada dadewa ba.
A cikin yunkurin nasu na gamawa da ‘yan ta’addan ne babban Hafsan sojan kasa Laftanar Janar Tukur Buratai ya kaddamar da rabon babura na musamman ga mayakan rundunar sojan kasa a ranar Larabar da ta gabata.

A wani labarin kuma, gwamnatin kasar Amurka ta mikawa majalisar dokokin kasar wani kuduri da ya kunshi hanyoyin da kasar za ta bi ta taimakawa Nijeriya don magance matsalar Boko Haram da ya addabi yankin Arewa maso gabashin kasar nan.
Majiyarmu tq Premium Times ta ruwaito cewar Amurka ta gano wasu daga cikin abubuwan da suka sanya kungiyar Boko Haram yin karfi sun hada da tsananin talauci daya addabi yankin Arewa maso Gabas da kuma rashin adalcin shugabanni.
Gwamnatin kasar Amurka ta yi wa dokar mai lamba S.1632 suna ‘dokar samar da hadin gwiwa don magance barazanar kungiyar Boko Haram’ wanda shugaban kasa mai barin gado Barack Obama ya rattaba hannu a kai.
Wadannan sune baburan da aka rabawa sojojin.

You may also like