
Asalin hoton, BBC Sport
Dan wasan tsakiyar Sfaniya da Barcelona Sergio Busquets ya sanar da cewa ya yi ritaya daga buga wa kasarsa kwallo.
Mai shekaru 34 ya ci kofin duniya a 2010 da kuma kofin nahiyar Turai a 2012, kuma shi ne kyaftin din kasarsa a Qatar 2022 kafin Maroko ta cire su a zagayen kasashe 16.
”Bayan shekaru 15 da wasanni 143, lokaci ya yi da zan yi bankwana da buga wa kasata kwallo”, in ji Busquets, kamar yadda ya rubuta a shafukansa na sada zumunta.
Ya kara da cewa abun alfahari ne da na wakilci kasata na kuma taimaka mata ta kai babban mataki.”
Basquets ne dan wasa na karshe da ya yi ritaya a tsakiyar Barcelona da ta yi suna, da ta hada da kocin Barcelona Xavi da kuma Iniesta.
Ya kuma yi ilahirin rayuwarsa ta kwallon kafa a matsayin kwararre a Barcelona, inda ya ci kofuna da dama da suka hada da kofunan La Liga takwas da kuma na Zakarun Turai uku.