CBN Ta Bai Wa Matasa 310 Miliyoyin Naira Da Habaka Sana’unsu


 

Babban Bankin Nijeriya CBN da hadin gwiwar Heritage Bank a jiya Alhamis, sun raba naira miliyan 93 ga matasa masu kananan kasuwanci har 310 a birnin tarayya Abuja

 

Gwamnan Babban Bankin ta kasa, Mista Godwin Emefiele, wanda mataimakinsa kan harkokin kasuwanci da masana’antu Alhaji Suleiman Barau ya wakilta, ya mika cakin naira milyan 3 ga kowane matashin dan kasuwa

 

An gudanar da wannan tsarin ne a karkashin wani tsari na Babban Bankin kan Tallafawa Matasa Masu kananan Masana’antu da ake kira da YEDP tare da hadin gwiwar Hukumar Bautar Kasa ta Nijeriya NYSC

Mista Emefiele, ta bakin Alhaji Barau ya bayyana cewa shirin YEDP shiri ne da zai yunkura wajen zaburar da matasa masu son cin gashin kansu ta hanyar kasuwanci da masana’antu, ta yadda shirin zai samar da sama da matasa masu burin kafa masana’antu akalla miliyan 1 kafin shekarar 2020

 

Ya cigaba da cewa, wannan tsari na matasa ne zalla daga dalibai zuwa masu bautar kasa, zuwa masu wata basira ko aikin hannu na daban wadanda shekarunsu bai wuce shekaru 18 zuwa 35 ba. Kuma don saukaka harkar jinginar samun bashin, bankin zai karbi takardar shaidar NYSC, ko samun sa hannun wani fitaccen mutum a matsayin shaida ko ma wata kadara a matsayin jingina

Alhaji Barau ya cigaba da cewa bankunan Sterling da na Fidelity su ma za su bi sahun Heritage wajen bada irin wannan tallafi na tsarin YEDP.

Ya cigaba da cewa, CBN na jan hankalin matasa da su shiga wannan tsari wanda zai basu damar samun aikin yi kai tsaye

You may also like