CBN ya ba da kai kan kara yawan kuɗaɗen da za a dinga cirewa daga bankinaira

Babban bankin Najeriya CBN, ya yi amai ya lashe kan matakinsa na ƙayyade yawan kuɗaɗen da za a dinga cirewa daga bankuna a ƙasar.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, CBN ya ce a yanzu ɗaiɗaikun mutane za su iya cire kudi har naira 500,000 yayin da kamfanoni kuma za su iya cire naira miliyan biyar duk mako.

Wannan sabon matakin na CBN na zuwa ne kwana 15 bayan fitar da dokar farko da ta ƙayyade yawan kuɗaden da mutane za su iya cirewa daga bankunan a duk sati.

Tun da farkon CBN ya ce ɗaiɗaikun mutane za su iya cire naira 100,000 ne su kuma kamfanoni za su cire naira 500,00 ne kawai a duk mako.Source link


Like it? Share with your friends!

1

You may also like