CBN ya shawarci masu mu’amala da bankuna da su dena karbar lalatattun takarda kudi daga hannun bankuna.


Babban Bankin Najeriya, CBN ya ce kamata ya yi kwastomomi su rika bukatar sabbin takardun kudin Naira daga bankunan kasuwanci da suke mu’amala da su kana su ki karbar kudaden da suka yayyage.

Da yake tattaunawa da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN ranar Alhamis a Lagos, Isacc Okorafor mai magana da yawun CBN ya ce bankunan kasuwanci suna yin zagon kasa ga kokarin babban bankin na maye gurbin tsofaffin kudaden da kuma sabbi.

Babban bankin ya taba yin ikirari makamancin haka cikin watan Fabrairu.

Okorafor, ya ce babban bankin na sane da abin da yake faruwa kuma ya dauki matakai daban-daban domin maganin matsalar yagaggun kudi da suke zagawa a hannun mutane.

Ya ce babban bankin ya dauki wani sabon tsari na janye kudaden daga hannun mutane batare da yin amfani da bankunan kasuwanci ba.

Kuma tuni wannan sabon tsari ya fara aiki a babban birnin tarayya Abuja, Kano da kuma Kaduna.

Tsarin ya kunshi yin amfani da kungiyoyin yan kasuwa wajen tattara yagaggun kudaden.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like