
Asalin hoton, Reuters
An dai sake fasalin takardun Naira 200, 500 da kuma 1000
A ranar Alhamis ne za a fara amfani da sabbin takardun kudi da aka sauya a karon farko cikin shekaru 20 a Najeriya.
Hukumomi a kasar sun ce sun dauki matakin sauya fasalin kudin ne domin magance matsalar tsaro, da samun damar mayar da garin kudi bankunan kasar.
Babban bankin Najeriya ya ce kashi 80 cikin 100 na kudin da ke hannun jama’a na wurin wasu tsirarun mutane.
CBN ya bukaci ‘yan Najeriya su gaggauta mayar da tsofaffin kudaden da suke hannunsu bankuna, domin a sauya musu da sabbin.
Ranar 31 ga watan Janairu ne wa’adin da hukumomi suka kayyade zai cika ga mutanen da aka bai wa umarnin mayar da tsofaffin kudin banki.
Yawancin ‘yan Najeriya na ganin kamata gwamnati ta mayar da hankali kan abubuwan da suka fi damun ‘yan kasa, kamar magance hauhawar farashin kayayyaki, maimakon sauya fasalin kudi.
Wannan sabon tsari dai ana ganin ‘yan siyasa ne za su fi kowa ji a jika, wadanda ake ganin suna shirin sayen kuri’u a babban zaben Najeriyar da za a yi a watan Fabrairun 2023.
Fara amfani da sabbin kudin na zuwa ne kusan makwanni uku gabanin fito da wani tsarin da CBN ya yi na kayyade adadin kudin da masu asusun ajiya na banki za su iya fitarwa a kowacce rana, ko aikewa wani asusun da kuma amfani da POS.
Adadin kudin da za a iya cirewa a kowanne mako bai wuce Naira 100,000, sai kuma kamfanoni da suke da ka’idar Naira 500,000. Lamarin da ke ci gaba da janyo zazzafar muhawara har a majalisun kasar.