
Wata taƙaddama ta barke tsakanin kungiyar manyan ma’aikatan mai ta PENGASSAN da kungiyar manyan dillalan man fetur a Najeriya kan tsadar da mai ke yi a ƙasar.
Kungiyar manyan ma’aikatan mai a Najeriya ta PENGASSAN ce dai ta buƙaci hukumomin tsaron kasar da su dakatar da dillalan man fetur a ƙasar daga boye mai don sayar da shi sama da farashin gwamnati.
Shugaban kungiyar na kasa Comrade Festus Osifo ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a Abuja.
Ya ce: “ƙarancin man fetur din da ake fama da shi a kasar da ya-ƙi-ci, ya-ƙi cinyewa, ya zama abin damuwa ga ‘yan Najeirya saboda yadda ya fi shafar su, inda suke sayen man fetur din fiye da ainihin farashin da gwamnatin ƙasar ke sayarwa.”
Osifo ya ce dillalan ba su da hujjar da za su ƙara farashin man fetur ba, ba su da ikon da za su yi ƙarin kudin man fetur din.
Ya zargi “gwamnati da nuna halin ko in kula kan matsalar, saboda shiru da ta yi kan batun.
Kungiyar ta PENGASSAN ta buƙaci hukumomin tsaron Najeirya da su gaggauta daukar matakin hukunta ma dillalan man.
“Muna buƙatar bangarorin tsaron Najeriya, musamman hukumar hana fasa-ƙauri ta Najeriya da ta shige da fice da su kawo ƙarshen fasa-ƙaurin da ake yi a ƙasashen Afirka.
Sai dai ƙungiyar ta manyan dillalan man fetur ta musanta zargin, inda ta ce laifin kungiyar manyan ma’aikata ne, kasancewar su ma’aikatan gwamnati da suka shigo harkar sayar da mai da ba nasu ba.
Shugaban ƙungiyar manayan dillalan man fetur na arewacin Najeriya Bashir Dan Mallan ya ce PEGASSAN na da hannun wajen tsadar da man fetur din ke yi a Najeriya, da yadda suka sa musu harajin da suka sanyawa masu dakon man.
“Mun fi so hukumomin tsaron ma su shigo, domin su fahimci wadan ke haifar da tsadar man fetur a Najeriya. duk motar da zata shigo sai sun nemi a basu wani abu akai.
Haka kuma ya musanta zargin cewar suna boye man fetur da su siyar da shi da tsada, inda yace da maganar tsada da mai ya yi suka ma zarge su da shi, wanda kowa ya san da tsada muke samo shi.
Najeriya ita ce ƙasar da ta fi kowacce arziƙin man fetur a Afirka, sai dai an shafe gwamman shekaru tana fama da samun matsalar ƙarancin man fetur akai-akai.
Hakan ya samo asali ne kan rashin matatun man fetur da ke cikin hayyancinsu a ƙasar.
Wannan dalili ne yasa tilas ƙasar ke sayen tataccen man fetur daga ƙasashen wajen da take sayar musu da ɗanyen.
Batun shirin gwamnati na janye bayar da tallafin mai yana yawan jawo tarnaƙi a wajen samar da man.