
Asalin hoton, Getty Images
Kocin Manchester United Erik ten Hag ya ce ya yi imanin cewa sayar da kungiyar abu ne mai kyau wanda kuma ya kamata.
Ya ce hakan kadai zai sa United ta iya shiga tsara kamar makwabciyarta Man City da kuma Newcastle.
Magoya bayan kungiyar ta Old Trafford sun sha yin bore don neman Iyalan Glazer su sayar da ita.
A wannan karon, mamallakan kungiyar sun ce za su yar da kwallon mangwaro su huta da kuda.
A 2005 ne iyalan Glazer suka sayi Manchester United kan kusan dala biliyan daya da rabi.
Ten Hag ya ce irin yadda gasar Firimiyar Ingila ke dada zafi, sayar da kungiyar zai samar mata da karin kudaden sayen sabbin ‘yan wasa.
Kuma hakan zai dawo da martabar kungiyar mafi lashe kofuna a gasar Premier League, in ji shi.
A ranar 27 ga wata ne Manchester United za ta kara da Nottingham Forest bayan dawowa daga hutun Gasar Kofin Duniya ta 2022 a Qatar.