A jiya Laraba, rundunar Sojin Nijeriya ta tabbatar da cewa ta ceto kimanin mutane 801 daga hannun mayakan Boko Haram a cikin makonni biyu.
Kwamandan rundunar ofireshon ‘ Lafiya Dole’, Lucky Irabor shi ya sanar da haka ga manema labarai a garin Maiduguri.
Ya ce an ceto mutanen ne tsakanin 23 ga watan Nuwamba da yanzu.
Ya kara da cewa sun kuma kama wasu daga cikin ‘yan Boko Haram din yayin da suke kokarin guduwa daga dajin Sambisa a sakamakon fatattakar da su da ake yi.
Haka kuma ya ce, a ranar 4 ga watan nan, rundunar tare da hadin gwiwar mayakan sa kai sun gano wasu mutane; maza 5 da mata da yara 29 yayin da suke dosar garin Goniri daga Kafa a jahar Borno.
Ya ce bayan da suka yi bincike akan mutanen ne suka gano cewa biyu daga cikinsu mayakan Boko Haram ne, wadanda ya ce tuni an mika ga rundunar ‘yan sanda.