Chadi ta raba gari da jakadan Jamus | Labarai | DWJakadan jamus a kasar Chadi ya fice daga babban birnin kasar a yammacin jiya, jim kadan bayan da fadar mulki ta birnin N’Djamena, ta bukaci Jan Christian Gordon Kricke ya fice mata daga kasa a cikin sa’o’i 24.

Ma’aikatar harkoklin wajen Chadin ce ta tabbatar da haka a yau a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakinta Aziz Mahamat Saleh. Chadi ta zargi jakadan Jamus din da katsalandan a cikin harkokinta na cikin gida, abinda ta kira ka iya gurbata zaman takewa a tsakanin ‘yan kasar.

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like