Chaina:Mutane 40 sun mutu a rugujewar gini


 

 

Rugujewar wani dogon gini da ake aiki a kan shi, ya haddasa mutuwar mutane 40 a birnin Fengcheng da ke Gabashin kasar Chaina.

China Einsturz einer Bauplattform im Kraftwerk Fengcheng (picture-alliance/dpa/Fan Cunbao)

Wani gini da ya ruguje yayin da ake aikinsa a wata cibiyar samar da wutar lantarki a kasar Chaina, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 40 a wannan Alhamis din a yankin Jiangxi da ke Gabashin kasar a cewar kanfanin dillancin labaran kasar ta Chine nouvelle.

Da misalin karfe 7:00 na safiya ne agogon kasar Chaina hadarin ya aufku a birnin Fengcheng yayin da ake gina wani dogon bene, inda masu aikin ceto suka isa wurin domin bayar da agajin gaggawa.

Irin wannan hadari dai na cikin kanfanoni a kasar ta Chaina ya zama ruwan dare gama duniya, inda a shekarar da ta gabata, wasu ababe da suka fashe a birnin Tianjin da ke yankin Arewa maso Gabashin kasar, suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 170, kuma Shugaban kasar ta Sin Xi Jinping ya sha alwashin cewa hukumomin kasar za su dauki darasi kan iri-irin wadannan hadaruka da ke afkuwa.

You may also like