
Asalin hoton, Getty Images
AC Milan za ta kara da Tottenham a San Siro a Champions League ranar Talata a wasan ‘yan 16 da suka rage a gasar.
Tottenham tana ta biyar a teburin Premier da maki 39, ita kuwa Milan mai maki 41 tana ta shida a teburin Serie A.
Milan tana da kofin zakarun Turai bakwai jimilla, ita kuwa Tottenham na fatan daukar na farko a tarihi.
Antonio Conte ya koma jan ragamar Tottenham bayan jinya da ya yi, sai dai kungiyar ta sha kashi da ci 4-1 a hannun Leicester City a Premier ranar Asabar.
Kungiyar da ke buga Premier League za ta kara da Milan ba tare da kyaftin Hugo Lloris ba, wanda ke jinyar wata biyu.
An dakatar da Pierre-Emile Hojbjerg, yayin da Rodrigo Bentancur zai yi jinya zuwa karshen kakar bana.
Dan wasan tawagar Uruguay ya ji rauni a fafatawar da Leicester City ta casa Tottenham a King Power.
Wani dan kwallon Tottenham da ba zai yi mata wasan da ta ziyarci Italiya shi ne Yves Bissouma, wanda ke bukatar likitoci su yi masa aiki a kafarsa ta dama.
Saboda haka Conte ya ce zai yi amfani da matashin dan wasa mai shekara 22, Oliver Skipp da Pape Matar Sarr, mai shekara 20 a gurbin tsakiya.
Wannan shi ne wasa na biyar da za su fafata a tsakaninsu a gasar Zakarun Turai, inda Tottenham ta ci biyu da canjaras biyu.
Wasannnin da suka buga a ttsakaninsu: