Charley Boy Zai Fara Zanga-Zangar Neman A Taso Keyar Diezani Gida Daga Kasar Birtaniya Charles Oputa da aka fi sani da Charley Boy a ranar Litinin zai jagoranci zanga-zanga zuwa ofishin hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC domin neman a taso keyar tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison Madueke gida Najeriya daga kasar Birtaniya.

 Boy,Ya bayyana haka a wata sanarwa da ya sanya hannu shi da Deji Adeyanju,a ranar Alhamis.

A kwanakin baya ya jagoranci zanga-zangar neman Buhari ya dawo gida daga jinyar da yake a birnin London ko kuma ya sauka daga mulki.

A daya daga cikin ranar da yake gudanar da zanga-zangar wasu bata gari sun kai masa hari a kasuwar Wuse dake Abuja. 

Alisson Maduaeke na da hannu a cikin ba dakalar cin hanci ta makudan  kudi da dama har takai ga gwamnati ta kwace wasu daga cikin gidajen da ta mallaka na biliyoyin naira.

Amma tsohuwar ministan ta dage kan cewa bata aikata wani laifi ba kuma kadarorin da aka karba duk ba mallakinta bane. 

 

You may also like