Chelsea da Saudiyya na zawarcin Mourinho, PSG za ta rabu da Messi da Neymar



Jose Mourinho

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta tuntubi tsohon kociyanta kuma na Roma a yanzu Jose Mourinho domin ya sake komawa kungiyar ta Stamford Bridge a karo na uku. (Relevo)

Haka kuma Mourinhon ya samu tayin tafiya Saudiyya aiki na shekara biyu inda za a ba shi albashin yuro miliyan 120. (Corriere dello Sport )

Har-wa-yau Chelsean na neman sayen dan gaban Benfica Goncalo Ramos, dan Portugal mai shekara 21. (Football Insider)

Inter Milan na son kulla wata sabuwar yarjejeniya da dan bayanta na Italiya Alessandro Bastoni, yayin da Manchester City ke nuna sha’awarta a kan dan wasan mai shekara 23. (Calciomercato)



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like