Chelsea na daf da nada Lampard kocin rikon kwarya



Frank Lampard

Asalin hoton, Getty Images

Frank Lampard na daf da zama kociyan Chelsea na rikon kwarya zuwa karshen kakar nan, bayan shekara biyu da ta kore shi.

Lampard bai da wata kungiya da yake jan ragama a yanzu haka, tun bayan da Everton ta sallame shi a Janairu, kasa da shekara daya a Goodison Park.

Tsohon dan wasan Chelsea ya horar da kungiyar tsakanin Yulin 2019 zuwa Janairun 2021, wanda Thomas Tuchel ya maye gurbinsa.

Ranar Lahadi Chelsea ta raba gari da Graham Potter, wanda ya maye gurbin Tuchel a Stamford Bridge.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like