Chelsea na zawarcin Gavi, Liverpool na son dauko Mount, Newcastle na hararo Harvey



Mason Mount

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta tattauna da ejan ɗin dan wasan tsakiya na Sifaniya Gavi, mai shekara18, kan musayar shi ba tare da ko kwabo ba daga Barcelona a kakar wasanni. (AS – in Spanish)

Liverpool na da aniyar dauko dan wasan Chelsea Mason Mount, mai shekara 24, an fara batun dan wasan tsakiyar a kakar da muke ciki, bayan janyewa daga dauko dan wasan Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, daga Borussia Dortmund. (Football.London)

Bayern Munich na duba yiwuwar daukar dan wasan Napoli, kuma mai kai hari na Nigeria Victor Osimhen, mai shekara 24, wanda ke son komawa bangaren Bundesliga. (Sky Germany – in German)

Tsohon kocin River Plate Marcelo Gallardo na son aikin dindindin a matsayin manajan kungiyar Chelsea. (UOL – in Portuguese)



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like