Chelsea ta dauko dan Ivory Coast David Datro Fofana



s

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta sanar da kulla yarjejeniya da dan kwallon Ivory Coast David Datro Fofana daga kungiyar Molde FK ta Norway.

Fofana mai shekaru 20 da haihuwa, ya ci kwallo 15 a wasanni 24 da ya buga gasar kwallon Norway.

Chelsea na karancin ‘yan wasan gaba, bayan Armando Broja ya ji rauni kuma zai yi jinyar lokaci mai tsawo.

“Chelsea ta kammala yarjejeniya da Molde FK game da sayen David Datro Fofana. Zai hade da mu a ranar 1 ga watan Janairu,” in ji Sanarwar da Chelsea ta fitar.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like