
Asalin hoton, Getty Images
Mai kungiyar Chelsea Todd Boehly ya gana da Shugaban Paris St-Germain president Nasser Al-Khelaifi a Paris domin tattaunawa game da sayen dan wasan gaba na Brazil Neymar mai shekara 31. (Le Parisien – in French)
Arsenal na bibiyar dan wasan gaba na Manchester United, Marcus Rashford, 25, dai-dai lokacin da ake da rashin tabbas kan kwantiraginsa a Old Trafford. (Football Insider)
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya nemi kulob din ya sayi dan wasan tsakiya na Spaniya Martin Zubimendi mai shekara 24 daga Real Sociedad. (Sport – in Spanish)
Kocin Barcelona Xavi ya ce mai bugawa Netherlands tsakiya Frenkie de Jong, 25, bai so ya shiga Manchester United ba a waccan bazarar inda kulob din biyu ke shirin haduwa a gasar Europa Europa League. (Sun)
Barca ta kulla yarjejeniya da LA Galaxy domin sayen dan wasan Mexico mai shekara 21 Julian Araujo har zuwa Yunin 2026. (Fabrizio Romano)
Araujo zai isa Barcelona ranar Alhamis domin fara atisaye da kungiyar ta Spaniya. (ESPN)
Tottenham na zawarcin mai tsaron baya a Ecuador Piero Hincapie 21 daga Bayer Leverkusen. (Caught Offside)
Aston Villa na iya duba tayin da ake mata kan golan Argentina Emiliano Martinez, 30, domin ta samu damar taimaka wa kungiyar ta iya saye da cefanar da yan wasa. (Mail)
Dan wasan Portugal Joao Cancelo, 28, ya karyata rade-radin da ake yi game da sabani tsakaninsa da kocin Manchester City Pep Guardiola kafin ya koma Bayern Munich a matsayin aro. (Mundo Deportivo, via Mirror)
Mauricio Pochettino na iya koma wa Tottenham a matsayin koci don maye gurbin Antonio Conte da ke fuskantar matsin lamba. (TalkSPORT)
Chelsea da Liverpool da Manchester City da Manchester United da Newcastle sun tuntubi Independiente del Valle na Ecuador kan matashin dan wasan tsakiya mai shekara 15 Kendry Paez. (90min)