
Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta sha gaba a farautar dan wasan Najeriya da ke taka leda a Napoli Victor Osimhen, mai shekara 24, a wannan kaka. (Evening Standard)
Chelsea ta kuma matsa kaimi kan saye dan wasan Barcelona da Sifaniya Alejandro Balde, mai shekara 19, domin maye gurbin dan wasan su na Ingila Ben Chilwell, mai shekara 26. (Sport – in Spanish)
Bayern Munich na son dauko dan wasan Chelsea Kai Havertz, mai shekara 23, domin sake hadewa da tsohon kocinsa Thomas Tuchel. (90min)
Paris St-Germain ta fadawa Lionel Messi za ta biya ko nawa domin tabbatar da cewa dan wasan na Argentina bai bar kungiyar ba, yayinda ake rade-radin yiwuwar ya koma Barcelona.(Mundo Deportivo)
Arsenal ta matsu ta saye dan wasan Real Madrid mai buga tsakiya Aurelien Tchouameni wanda ita ma Liverpool ke hari. (El Nacional – in Catalan)
Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce kungiyar ta kamala shirye-shiryen dauko manyan ‘yan wasanni domin inganta wasanninta a sabuwar kaka. (Mirror)
Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron baya a Ingila Luke Shaw, dan shekara 27, ya amince da sabon kwantiragin shekara hudu a Manchester United. (Athletic – subscription required)
Dan wasan Chelsea Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 33, na son komawa Barcelona, sai dai da alama ba a shirya sayar da shi ba a yanzu ba. (Sport – in Spanish)
Roma na duba yada za ta dauko mai tsaron raga a Manchester United David de Gea, da kwantiraginsa ke gab da karewa. (Fichajes – in Spanish)
Daniel Levy ba shi da niyyar sayar da ‘yan wasansa, yayinda shugaban Tottenham ke dana sanin sayar da Kyle Walker ga Manchester City a 2017. (Daily Mail)
Erik ten Hag zai yanke hukunci kan makomar ‘yan wasan Manchester United biyu Scott McTominay da Victor Lindelof, yayinda shi kuma dan wasan Scotland McTominay, ya ja hankalin Newcastle da kuma dan wasan Sweden Lindelof, mai shekara 28, da ya rikita Inter Milan da Atletico Madrid a watan Janairu. (Fabrizio Romano)
Dan wasan Crystal Palace da Ghana Jeffrey Schlupp, mai shekara 30, da Jordan Ayew, mai shekara 31, sun sanya hannu kan sabon kwantiragi. (Athletic – subscription required)