Chelsea za ta yi wa Arsenal shigar sauri kan Mudryk, Depay na son kome Manchester Utd



mudryk

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea na neman yi wa Arsenal kancal a cinikin matashin dan wasan Shakhtar Donetsk Mykhailo Mudryk, dan Ukraine, duk da cewa tuni Gunners din sun daidaita da dan wasan mai shekara 21, inda Stanford Bridge ke son saye shi. (Sun)

Ga alama Chelsean tana jan kafa wajen biyan yuro miliyan 120 na sakin matashin dan wasan tsakiya na Argentina Enzo Fernandez, kamar yadda kwantiraginsa da Benfica, ya tanada, kuma kungiyar tasa na son lalle sai an biya kudin gaba daya kafin ta sake shi. (Telegraph)

Alamu na nuna cewa dan wasan tsakiya na Holland Memphis Depay na shirin sake komawa Manchester United amma kuma kociyan Barcelona Xavi yana son ya ci gaba da zama a Nou Camp. (Metro)

Duk da kokarin da dan bayan Manchester United Aaron Wan-Bissaka ke yi a yanzu, kila ta sayar da dan Ingilar a watan Janairu. (Athletic)



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like