
Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron bayan Chelsea, Ben Chilwell ya tsawaita kwantiragin ci gaba da taka leda a Stamford Bridge zuwa karshen kakar 2027.
Dan kwallon tawagar Ingila, mai shekara 26, ya yi wa Chelsea karawa 80 a dukkan fafatawa, tun bayan da ya koma kungiyar daga Leicester City a 2020.
Mai tsaron bayan yana daga cikin ‘yan wasan Chelsea da suka lashe Champions League a 2021, bayan doke Manchester City a karawar karshe.
Chilwell, wanda ya buga wa Ingila wasa 18 ya yi wa Chelsea fafatawa 25 a bana a dukkan karawa da cin kwallo biyu.
Chelsea wadda ke mataki na 11 a gasar Premier a bana ta nada Frank Lampard a matakin rikon kwarya zuwa karshen kakar nan, bayan da ta kori Graham Potter.
Ranar Laraba, Chelsea za ta kara da Real Madrid a Sifaniya a wasan farko zagayen quater finals a Champions League.