China na son a warware rikicin Ukraine | Labarai | DWWata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen China ta fidda ta rawaito shugaban na China na cewar ya kyautu bangarorin biyu da ke kai ruwa rana da juna su hau teburin tattaunawa don kawo karshen rikicin da ke wakana tsakaninsu.

Shugaban na China dai a baya-bayan nan na kokari wajen ganin manyan kasashen duniya da ke rikici da juna sun mayar da wukakensu cikin kube, don ko a ‘yan kwanakin da suka gabata ya shiga tsakanin Iran da Saudiyya wanda hakan ya sa suka fara shirin maido da huldar diflomasiyya tsakaninsu.
 

Source link


Like it? Share with your friends!

1

You may also like