Sojin ruwan China sun kama wani jirgin ruwan karkashin teku na Amurka a tekun Kudancin China wanda ake rigima a kansa.
Kakakin ma’aikatar tsaro ta Pentagon Laftanar Kanal Jeff Davis ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne ga wani jirginsu mai bincike a karkashin teku.
Ya ce, sojin China sun kama jirgin a gaban sojin Amurka wanda ya ke tattara bayanan kimiyya domin amfanin kasar da ya fito.
Davis ya ce, sun mika korafi ga kasar China tare da neman a dawo musu da jirgin nasu.
China da makotanta na rikici game da tekun Kudancin Chinan wanda ke dauke da arziki da dama.
Gwamnatin China dai ta samar da tsibirai a kan tekun tare da samar da sansanin soji don sanya idanu da tsare tekun.
Amma Amurka da kasashen yankin na adawa da wannan mataki da China ta dauka.