Chioma Ta Zama Macen Da Tafi Kowacce Kyau A Najeriya An zabi Chioma Obiadi a matsayin sarauniyar kyau ta Najeriya ta bana bayan gasar da aka gudanar karo na 40 a birnin Lagos.
Mis Obiadi, wacce ‘yar asalin jihar Anambra ce, ta doke Mis Blessing Obila daga Ebonyi, yayin da Mis Shade daga Kwara ta zo ta uku.
Kamfanin dillancin labarai (NAN), ya ruwaito cewa an fara gasar ne tun shekarar 1957.

Mata 38 ne suka shiga gasar bana daga jihohin kasar da kuma birnin tarayya Abuja, wacce aka gudanar a otel din Eko Hotel and Suite da ke Lagos.
An fara tankade ‘yan takara daga 38 zuwa 10 kafin su koma uku.

Kamfanin jaridar Daily Times ne ke shirya gasar tare da hadin gwiwar wasu kamfanoni masu zaman kansu.
Da ta ke magana da NAN, wacce ta zo ta biyu Obila, wacce ta yi karatu a jami’ar jihar Akwa Ibom, ta bayyana jin dadinta game da nasarar da ta samu.
Rahotanni sun ce taron ya yi armashi inda ya samu halartar masu kade-kade da raye-raye daga sassan kasar da dama, cikin har da matar da ta fara lashe kyautar Misis Grace Oyelude.

You may also like