Christiano Ronaldo,dan wasan gaba na kungiyar Kwallon kafa ta Real Madrid,shine dan wasa da yafi kowanne dan wasa samun kudi a duniya cikin shekaru biyu a Jere a cewar mujallar Forbes.
Hakan na kunshe ne a cikin jerin sunayen yan wasan da sukafi samun kudi da mujallar take fitarwa duk shekara.
Wanne dai karo na biyu da dan wasan yake kasancewa na daya a jerin sunayen da mujallar kasuwancin take fitarwa a duk shekara.
Dan wasan ya samu zunzurutun kudi har dalar Amurika miliyan $93 daga albashi da kuma tallan kayayyaki.
Kudin da dan wasan mai shekaru 32 ya samu a wannan shekara sun karu da dala miliyan biyar idan aka kwatanta da abinda ya samu a shekarar data gabata.
Dan wasan kwallon kafa na kungiyar Barcelona,Lionel Messi shine a mataki na uku.