Cigiya Daga Ofishin Hukumar Hisba Ta Jihar Kano Wannan bawan Allah an gan shi ne yana ta gararamba a gari kuma an tambaye shi ya kasa tantance inda ya fito. Saidai ya bayyana sunansa a matsayin Adamu.

Don haka ake kira ga jama’a da duk wanda ya san shi ko ya san ‘yan uwansa sai ya tuntubi Hedikwatar Hukumar Hisba ta jihar Kano dake unguwar Sharada.
Ana bukatar a yada sanarwar.

You may also like