Tun ranar 31 ga Yulin 2016 Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya cika shekaru 55 da haihuwa, kuma a ci gaba da murnar, Sarki adali mai ilimin addini da na zamani ya tallafawa yara marayu har guda 100 ya da duba lafiyarsu tare da ba su magani.
- Tarihinsa:
Sarkn Kano da ne ga Marigayi Ciroma Aminu, kuma jikan Marigayi Muhammadu Sanusi ba I, Sarkin Kano na 10, ya gaji sarauta gaba da baya, watau ya shige shige gidan magabatansa wato gidan Dabo.
Idan aka yi duba da irin yadda ya samu ilmin addinin Musulunci da na zamani. Sarki Muhammadu Sanusi II, bayan digirinsa na farko da na biyu a kan fannin tattalin arzikin kasa a Jami`ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarun 1981 da 1983, kuma ya kama aikin koyarwa a dai Jami’ar ta Ahmadu Bello a shekarar 1983 zuwa 1985. Ya kuma garzaya kasar Sudan inda ya yi karatun digirin farko a fannin shari’a da addinin Musulunci.
Ya fara aikin banki da ya shahara a ya aiki da Bankin ICON Merchant Bank a shekarar 1985 har zuwa 1997. Daga nan ya tafi bankin UBA, inda ya zauna har zuwa 2005. Ya bar bankin yana matsayin Janar Manaja, inda ya tafi First Bank a matsayin Babban Daraktan mai kula da sashen bada rance da taurin bashi, fannin da Sarki Muhammadu Sanusi II, ya fi kwarewa. Kuma ya zama Manajin Daraktan Rukunnan Bankin First Bank din, kuma shi ne dan Arewa na farko da ya taba rike irin wannan mukami a tsawon tarihin Bankin na sama da shekara 100, da kafuwa.
Ya zama Gwamnan Babban Bankin kasa a cikin watan Yunin 2010, shigarsa Babban Banki ke da wuya, ya iya gano cewa kusan Bankunan kasuwancin 1asar 15, daga cikin 25, da ake da su sun fara suma, biyar daga cikinsu suna bukatar agajin gaggawa, bisa ga irin yadda hukumomin gudanarwarsu da na zartaswa, sun yi sama da fadi da bilyoyin kudadensu walau ta hanyar bai wa kawunansu rance ko yin sama da fadi iri-iri.
Bayan ya tallafa masu ya kuma sanya an gurfanar da irin wadancan manyan darayin zaune, don karbo kudaden jama’a da suka wawure, wasu ma har da dauri. Wannan aiki na gyaran Bankuna ya batawa mutanen shiyyar Kudu Maso Yamma da na shiyyar Kudu Maso Kudu rai matuka saboda su ya fi shafa, don haka suka mike haikan suna yakar Gwamnan Babban Banki, musamman ta kafofin yada labarai. Amma da rana daya Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Dr. Muhammadu Sanusi ll bai taba saurarawa ba, ko yanzu idan an duba tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan da ya kasance mugun labari ga kusan duk ‘yan kasa.
A cikin irin waccan gwagwarmayar tabbatar da an yi komai cikin kamanta gaskiya da adalci, inda sarki a shekarar 2013, ya bankado bahallatsar sace makudan kudaden man fetur har Dalar Amurka bilyan 20 a hannun kamfanin man fetur na NNPC. Wannan fallasa ta yi matukar ta da hankalin tsohon Shugaban kasa Dakta Goodluck Jonathan, wanda ya nemi lalle sai Sarkin Kano ya janye, hakan ta sanya ya rage watanni hudu Gwamnan Babban Bankin ya kammala wa’adinsa na shekaru biyar, Shugaba Jonathan ya dakatar da shi.
Allah kuma cikin ikonsa kwana biyu da mutuwar Marigayi mai martaba sarki Ado, A ranar 08-06-15, Allah ya bawa Mai martaba Sarki Alh. Dr. Muhammadu Sanusi ll karagar sarautar Kano. Abin da ya fara yi shi ne babban aikin da ya fara kuma har yanzu yake kai shi ne dinke barakar zumunci tsakaninsa da dukkan ‘yan uwansa musamman na cikin gidan Dabo, ta hanyar jawo wadanda suke adawa da shi cewa gida na kowa ne. Kuma shi mulki na Allah ne shi ke bada shi ga wanda ya so a lokacin da ya so.
Mai martaba San Kano, ya kuma bullo da wasu manya-manyan ayyuka da zasu kara inganta rayuwar talakawansa, ya duba yanayin taswirar gine-ginen gidan sarautar da kuma irin halin da fadawansa da duk masu yiwa masarautar hidima ke ciki musamman batun gyaran albashi.
Sannan bai jima da zama sarki ba, watan azumin ya kama shekaru biyu da suka gabata. Mai martaba Sarki ya kai ziyara gidajen kangararru biyu da suke cikin birnin kano, wato Kurmawa da Goron Dutse, inda wasu fursunonin suka samu tagomashi daga hannunsa sakamakon ‘yantar da wasu fursunoni har kusan mutane 40 a gidajen fursunonin guda biyu kan kudin da ya haura naira miliyan bakwai, abun da ya jawowa sarki farin jini a idanun mutanen Kano dama na jihohin Nijeriya baki daya, duba da irin yadda jama’a ke ganin shi a irin wani sabon hawa karagar sarautar Kano.
Kuma nagartar Sarki ta samo asali ne daga ilminsa domin sarki Allah ya bashi tsantsar ilmin Adinin Musulinci da na yin shugabancin al’umma domin har tafsiri ya ke yi wanda ake ganin ya gaji kakansa Sa Muhammadu Sanusi I, (Allah ya yi masa rahama) sannan kuma a bangaren ilmin zamani daman wannan ba ya bukatar jawabi domin wanda duk aka nada a matsayin gwamnan babban bankin kasa ko shakka babu ka san batun ilmin zamanin ba a magana, haka wadanda suka taso da sarki suna cewa a bangaran ilmi Allah Ya yi masa baiwa wadda sai dai a yi addu’a kurum. Kuma wani daga cikin abokan sarki ya taba fada min cewar a tsarin tafiyar da harkoki irin na yau da kullum ga Mai martaba, akwai bukatar a fahimce shi sosai, domin idan ka fahimce shi mutum ne shi mai saukin kai. Amma gaskiya sai mutun ya nutsu ya yi nazari zai gano shi; ga shi mutum ne mai hangen nesa, domin shi ne sarki na farko a tarihin kasar Hausa da ya fuskanci babbar barazanar da ta zama labari mafi tasiri, duk da har yanzu akwai mutane da dama da basu fuskanci halayan sarki ba.
Idan Allah ya baka wani mukami ko shugabancin al’umma sai abin da ka ji ko ka gani, amma shi saboda ilminsa irin wasu kananan maganganu ba su gabansa,
Akidar da Sarki Muhammadu Sunusi II yake da ita ta soyayyar al’ummar Kano, ya zama na malamai da sarakuna, attajira ga uwa uba talakawa shi yasa ake yi masa lakabi sarkin sarakuna Arewacin Nijeriya.