Cikin kwanaki biyu yan majalisar wakilai biyu sun fice daga jam’iyar PDP zuwa APC


Johnson Agbonayinma, wakili a majalisar wakilai ta tarayya da aka tsaba karkashin jami’iyar PDP ya sauya sheka zuwa jam’iyar APC mai mulki. 

An sanar da sauya shekar tasa cikin wata wasika da kakakin majalisar Yakubu Dogara ya karanta  yayin zaman majalisar na ranar Alhamis.

Ya zargi PDP da rufe masa kofa shida sauran magoya bayan tsohon shugaban jam’iyyar Ali Modu Sharif.

Shine wakili na biyu dan jam’iyar PDP da ya sauya sheka cikin makon da muke ciki.

Mataimakin gwamnan jihar Edo Philip shuaibu ya halarci zaman majalisar na yau domin sheda yadda sauya shekar zata kasance.

Sauya shekar ta Agbonayinma na zuwa ne kwanaki biyu bayan da  wakili Nnanna Igbokwe daga jihar Imo ya  sauya sheka zuwa jam’iyar APC.

Agbonayinma shine wakili na takwas  a jerin yan majalisar wakilai ta tarayya ya’yan jam’iyyar PDP da suka sauya shekar zuwa APC.

You may also like