Majalisar Dinkin Dinkin ta ce ana yi wa kananan yara mata fyade a Cote d’Ivoire ba tare da an hukunta masu aikata laifin ba saboda an dauki laifin ba wani abu bane.
Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya yace cikin mata uku da aka yi wa fyade a Cote d’Voire biyu daga cikinsu kananan yara ne.
Rahoton ya ce an yi wa mata fyade kimanin 1,130 tsakanin 2012 zuwa 2015.
Sannan rahoton ya ce matsalar na ci gaba da karuwa a yanzu saboda yadda yaran da aka yiwa fyade ke yin shiru don kunya ko tsoron bacin sunan gidansu da kuma rashin tabbas ga tsarin shari’ar kasar.
Wani dan rajin kare hakkin bil’adama a Cote d’Ivoire Jean Claude Kobena ya ce mafi yawancin mutane a Cote d’Ivoire sun dauki saduwa a matsayin bukata ga mata, al’amarin da ya sa suke cin zarafin kananan yara.
Sannan matsalar na karuwa ne sakamakon yadda yara ke yawo a titi saboda talauci.
Hukumar UNICEF ta bayyana damuwa akan matakan shari’a da mace zata bi kafin tabbatar da an yi mata fyade, inda sai ta yanki takardar shaida akan kudi cfa 50,000.