Cin Zarafin Mata Ta Hanyar Lalata A Jami’o’i Abin Tada Hankali Ne: BuhariWASHINGTON, D.C. – A shekarar 2019, BBC ta yi amfani da wani dan jaridan da ya yi shigar burtu wajen fallasa yadda ake cin zarafin mata a jami’o’i biyu a Najeriya da Ghana, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta kan matsalar “jima’i don maki”.

Masu suka dai sun ce ba a samu canji ba tun daga wancan lokaci, suna masu zargin gwamnati da gazawa wajen kawar da wannan mummunar dabi’a.

Wasu dalibai a jihar Legas

Wasu dalibai a jihar Legas

Sai dai Buhari ya shaida wa taron yaki da cin hanci da rashawa a Abuja cewa gwamnati ta damu, kuma hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta tana tuhumar cewa an aikata cin mutunci da cin zarafi ta hanyar lalata a cibiyoyin ilimi.

Shugaban dai bai bayar da wata kididdiga ba.

Buhari ya ce dalibai sun fito da harsunan da za su bayyana nau’ukan cin hanci da rashawa a makarantun jami’a.

“Akwai hanyar ware tsabar kudi don maki ko kuma jima’i don maki, jima’i don canza maki, rashin aikin jarrabawa, da sauransu,” in ji Buhari.

Ya ce “Tsarin na jima’i ya ɗauki kashi mai ban tsoro.”

Dalibai Na Rubuta Jarabawar JAMB A Najeriya

Dalibai Na Rubuta Jarabawar JAMB A Najeriya

Buhari ya ce sauran nau’o’in cin hanci da rashawa a jami’o’i sun hada da malaman makaranta da ke rubuta takardar shaidar kammala karatu ga dalibai a kan kudi, biyan albashi ga ma’aikatan da ba su da aiki da kuma malaman da ke daukar aiki na cikakken lokaci a makarantun ilimi fiye da daya.

Malaman jami’o’in gwamnati sun shafe fiye da watanni bakwai suna yajin aiki suna neman a kara musu albashi da alawus-alawus.

Buhari ya ce “wadanda ke shiga yajin aiki saboda wasu dalilan da ba su taka kara sun karya ba” daidai su ke da masu kawo cikas ga himmar da gwamnati ke bayar wa ga fannin ilimi.

-Reuters

You may also like