Cin zarafin yan Najeriya: Majalisar dattijai ta aika da tawaga mai ƙarfi zuwa Afirka ta kudu


 

Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki ne ya bayyana haka a yayin zaman majalisar a jiya Laraba, inda ya sanar da sunan mataimakin shugaban majalisar Sanata Ike Ekweranmadu a matsayin jagoran tawagar.

 

Ga cikakken sunayen yan tawagar:

Mataimakin shugaban majalisa Sanata Ike Ekweremadu

Shugaban masu rinjaye Sanata Ahmad Lawan

Mai tsawatarwa a majalisa Sanata Sola Adeyeye.

Mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin waje Sanata Shehu Sani

Sauran sun hada da:

Sanata Stella Oduah

Senator Magnus Abe

Senator Shaba Lafiaji.

idan za’a iya tunawa, a satin daya gabata ne wasu matasa suka fara far ma baki a kasar bakaken fata, inda suke zargin su da mamaye ayyukan dake kasar.

You may also like