Cinikin makamai- Najeriya ta maida martani akan dan Majalisar America. 


Gwamnatin Najeriya ta maida martani ga kiran da dan majalaisar dokokin Amurka, Tom Marino ya yi ga gwamnatin Barak Obama cewa ta dakatar da sayar wa Najeriya makamai.
Dan majalisar dai ya yi zargin cewa Najeriya ba ta amfani da makaman ta hanyar da ta dace.Ga alama kiran da dan majalisar dokokin Amurka ya yi,ya hassala gwamnatin Najeriya, idan aka yi la’akari da kalaman da ta yi amfani da su wajen mai da wannan martanin, duk kuwa da cewa gwamnatin shugaba Buharin na dasawa da gwamnatin Amurka.

Wata sanarwa dai ta ambato Ministan yada labaran Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, yana amfani da kausasan kalamai, yana cewa gwamnatin Najeriya ta ji takaicin wannan kira da dan majalisa Tom Marino ya yi cewa, Amurka ta dakatar da sayar wa Najeriya makamai, saboda Najeriyar na amfani da su wajen murkushe masu tsaurin ra’ayi, zargin da Ministan ya ce ba shi da tushe.

Gwamnatin Najeriyar ta ce ta yi mamakin yadda Tom Marino ya yi gaban kansa wajen yanke wannan hukunciba tare da tuntubar ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya ba.Kungiyoyin kare hakkin bil’adama dai sun sha zargin jami’an tsaron Najeriya da wuce gona da iri a yakin da suke yi da masu tada-kayar-baya, duk kuwa da cewa suna musantawa.

Ko da a baya-bayan nan ma wani kwamitin bincike da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa ya gabata rhinestone  da wani rahoton da ya zargi sojojin Najeriya da kashe daruruwan mabiya akidar shi’a, amma rundunar sojin kasar ta ce tana da ja.

Irin wannan zargi dai idan ya tabbata, zai yi mummunan tasiri ga gwamnatin Najeriya, saboda Amurka ka iya dakatar da sayar wa Najeriya makamai.Kuma daga nan kawayen Amurkan su za su bi sahu. 

Lamarin da zai iya haifar da koma-baya ga yakin da Najeriyar ke yi da masu tada-kayar-baya da sauran miyagun ayyuka a kasar.

You may also like