
Asalin hoton, BBC Sport
Real Madrid za ta fi mai da hankali wajen sa hannu kan yarjejeniya da ɗan wasan tsakiyar Borussia Dortmund daga ƙasar Ingila Jude Bellingham a cikin sabuwar shekara, inda matashin mai shekara 19 ke da niyyar zaɓar ƙungiyar ta ƙasar Sifaniya a kan Liverpool.
Bellingham zai zauna da Borussia Dortmund a cikin watan Janairu don tattaunawa kan batun makomar ƙwallonsa a gaba.
Manchester City na shirin miƙa ɗan wasansu na tsakiya ga AC Milan Jack Grealish, mai shekara 27, don karɓo ɗan wasan gaba mutumin ƙasar Portugal Rafael Leao, mai shekara 23.
Manchester United da Arsenal da kuma Chelsea sun shirya biyan Atletico Madrid fam miliyan takwas don ɗaukar aron ɗan wasanta na tsakiya daga Portugal mai shekara 23 Joao Felix.
Chelsea na nuna sha’awa kan ɗan wasan bayan Celtic daga ƙasar Croatia Josip Juranovic, mai shekara 27, a matsayin wanda zai maye gurbin ɗan wasanta Reece James mai shekara 23 da ya ji rauni.
Chelsea kuma tana ƙyalla ido kan ɗan wasan bayan Inter Milan mutumin ƙasar Netherlands Denzel Dumfries, sai dai matashin mai shekara 26 na cikin ‘yan wasan da Manchester United ke sa ran ɗauka.
Newcastle United sun yanke ƙauna ga burinsu na ɗauko ɗa wasan tsakiyar Chelsea mai shekara 31 Jorginho. (Football Insider)
Komai na tafiya daidai ga yunƙurin Arsenal na ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Lazio kuma mutumin ƙasar Serbia, Sergej Milinkovic-Savic, mai shekara 27.
Sai dai Shakhtar Donetsk ta ce sai an ajiye mata kimanin yuro miliyan 100 idan ana son ɗan wasan gefenta mutumin ƙasar Ukraine Mykhailo Mudryk, ɗan shekara 21, wanda ake ba da rahotannin cewa shi ne babban burin Arsenal.
Manchester United za ta mai da hankali ga lokacin shiga kasuwa don cefanen ‘yan wasa na ƙarshen kaka maimakon kashe kuɗaɗenta yanzu a watan Janairu.
Wani ɗan wasa da United ke hari shi ne ɗan bayan Napoli mutumin Koriya ta Kudu Kim Min-jae, mai shekara 26.
An ba da rahoton cewa ɗan wasan gaban Atletico Madrid kuma mutumin ƙasar Sifaniya Alvaro Morata, mai shekara 30, shi Manchester United ke da burin ɗaukowa a matsayin aro.
Bournemouth ta bi sahun Leicester City wajen bayyana sha’awa don ɗauko tsohon ɗan wasan gefen Chelsea da ke buga ƙwallo yanzu a Atalanta Jeremie Boga, don kuwa yanzu ana iya ɗaukar matashin mutumin ƙasar Ivory Coast mai shekara 25 a matsayin aro.
Ɗan wasan tsakiyar Newcastle Jonjo Shelvey na buƙatar buga wasa biyu kafin ya samu damar a ƙara masa kwanturagi, sai dai raunin da matashin mai shekara 30 ya ji a sharaɓa inda yake jinyar sama da mako takwas, ba zai ba shi wannan damar ba, ga shi kuma wata shida ne ya rage a yarjejeniyarsa ta yanzu.
Leeds na gab da cimma yarjejeniya da kaftin ɗin RB Salzburg kuma ɗan bayan Austria Maximilian Wober, mai shekara 24, sai dai su ma Everton sun nuna sha’awa.