Clinton: Bai kamata Trump ya zama shugaba ba saboda yana zagin Musulmai


 

 

 

‘Yan takarar shugaban kasar Amurka a zaben da za a yi a watan Nuwamba mai zuwa sun sake yin muhawara a bainar jama’a.

Trump ya nemi afuwar jama’a sakamakon wani tsaohon faifan bidiyo da aka nuna wanda ya taba yin wasu kalamai game da biyan haraji a Amurka.

Clinton ta ce, Trump bai cancanta ya zama shugaban kasa ba sabo yana zagin Musulmai, mata da kuma sauran baki ‘yan kasashen waje.

A yayin muhawarar an kuma mayar da hankali game da tsarin kula da lafiya na kasar Amurka.

Trump ya bayyana cewa, tsarin kula da lafiya da Obama ya kafa ba shi da kyau kwata-kwata kuma zai rushe shi tare da samar da sabon tsari, inda Clinton kuma ta ce, za ta ci gaba da aiki da wannan tsarin.

Wata mace Musulma da ta halarci wajen muhawarar ta tambayi ‘yan takarar game da batun kyamar Musulunci wato ‘Islamophobia’ a turanece.

Trump ya bayar da amsa da cewa, Islamophpbia wata babar matsala ce kuma ta haka ne za a gane aiyukan ‘yan ta’adda da masu tsattsauran ra’ayi.  Clinton kuma ta ce, Musulmai dole su sami sarari a idanuwa da kunnuwansu.

Game da kasar Siriya kuma Clinton ta ce tana goyon bayan kafa yankin zaman lafiya a kasar Siriya.

Amma Trump ya ce, babu wata kasa wai ita Siriya a yau. Kuma sakamakon Obama da Clinton kasar ta zama Iran da Rasha.

A ranar 19 ga watan Oktoba ‘yan takarar 2 za su sake fafatawa a bainar jama’a a jami’ar nevada.

You may also like