Clinton Ta Zargi Shugaban Hukumar FBI, Akan Yi Mata Kafar Ungulu


 

‘Yar takara data sha kaye a zaben shugaban kasa a Amurka, Hillary Cliton ta zargi shugaban hukumar leken asiri ta kasar, James Comey, da yi mata zagon kasa wanda ya yi ma yakin neman zaben ta illah sosai.

Misis Cliton wace ta bayyana hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho ga kwamitin yakin neman zaben ta ce akwai abubuwa da dama da suka zama sila na shan kayen ta a zaben da aka gudanar a ranar takwas ga watan nan.

Clinton ta ce sanarwar da Mista Comey ya yi  kan batun amfani da Email din ta a lokacin da ta ke Sakatariyar harkokin waje, kwanaki biyu gabanin zabe shi ya rage mata magoya baya.

Wadanan kalamen na Misis Cliton na zuwa ne a daidai lokacin da dubban Amurkawa ke ci gaba da boren kin amincewa da zababen shugaban kasar Donalt Trump.

A birnin New York ‘yan sanda sun yi kokari hana masu zanga-zangar isa dandalin Union, da wasu kuma na daban da suka tunkari gidan na Mista Trump ..

You may also like