Kungiyar Newcastle United, da kyaftin dinta Fabricio Coloccini, sun cimma yarjejeniyar kowa ya kama gabansa.
Coloccini mai tsaron baya, zai koma Argentina da murza-leda a kungiyar San Lorenzo.
Dan wasan mai shekara 34, ya buga wa Newcastle United wasanni 275, tun bayan da ya koma can da buga tamaula daga Deportivo La Coruna a shekarar 2008.
Newcastle United za ta buga gasar Championship ta bana, bayan da ta fadi daga gasar Premier da ta gabata.