
Asalin hoton, BBC Sport
Ga alama Tottenham Hotspur na shirin amincewa kocin kungiyar Antonio Conte mai shekara 53 ya bara kungiyar cikin makon nan, kuma ana sa rai tsohon dan wasan kungiyar Ryan Mason mai shekara 31 zai karbi ragamar horar da ‘yan wasan kungiyar daga nan zuwa karshen wannan kakar wasan. (Telegraph – subscription required)
Spurs na bukatar a biya ta fam miliyan 100 kan dan wasan gaban Ingila Harry Kane kafin ta amince ta rabu da dan wasan nata mai shekara 29 a karshen wannan kakar wasan. (Times – subscription required)
Manchester City kuwa na ganin za ta iya sayo Jude Bellingham, dan wasan tsakiya mai shekara 19 dan Ingila daga Borussia Dortmund, sai dai Real Madrid ma na da sha’awar sayensa. (ESPN)
Attajirin Birtaniyar nan Sir Jim Ratcliffe – wanda ke cikin jerin masu son sayen Manchester United – ya bayyana cewa ba zai biya kudin da suka zarce abin da hankali zai dauka wajen sayen kungiyar kwallon kafan ta United ba. (Wall Street Journal)
Arsenal na shirin tsawaita zaman Martin Odegaard, dan wasan. tsakiyarta mai shekara 24 har zuwa shekarar 2030 ta hanyar yi masa tayin sabuwar kwantiragi. (Football Transfers)
Newcastle United kuwa ta mayar da hankalinta ne kan sayo Scott McTominay daga Manchester United a karshen wannan kakar wasan, kuma dan wasan mai shekara 26 dan asalin kasar SCotland ya nuna sha;awarsa ta komawa can. (Telegraph – subscription required)
Chelsea za ta sayar da Edouard Mendy, golanta mai shekara 31 bayan da aka gaza kulla sabuwar yarjejniya kan tsawaita zamansa a kungiyar. (Football Insider)
Tsohon dan wasan Fulham, Andreas Pereira mai shekara 27 na cikin jerin ‘yan wasan da Chelsea ke zawarci, domin dan Brazil din zai iya maye gurbin Mason Mount, dan wasa mai shekara 24 – sai dai Atletico Madrid da PSG ma na rige-rigen sayen dan wasan. (ESPN)
Kyaftin din Sfaniya Sergio Busquets mai shekara 34 na duba yiwuwar komawa AMurka ko Saudiyya domin ci gaba da buga tamaula, sai dai za zai yanke hukuncin ci gaba da zamansa a Camp Nou ko kuma ya yi gaba yayin da ake shirin tafiya hutu a ‘yan kwanaki masu zuwa a yawanci gasar kwallon kafa na nahiyar Turai. (Mundo Deportivo – in Spanish)