Côte d’Ivoire: Dage shari’ar Simone Gbagbo


Wata kotu a Côte d’Ivoire ta dage sauraron shari’ar da ake wa uwargidan tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo wato Simone Gbagbo har zuwa 10 ga watan Oktoba..

 

Simone Gbagbo da mai gidanta tsohon shugaban kasar Cote d’Ivoire Laurent Gbagbo

 

 

 

Babban mai shigar da kara na gwamnatin Côte d’Ivoire Ali Yeo ya bayyana wa kotun da ke Abidjan babban birnin kasar cewar dage shari’ar ya biyo bayan bukatar hakan da lauyoyin Simone Gbagbo suka yi, bisa dalilin gajiya sosai da ta yi, wanda hakan ya sanya ba za ta iya halartar zaman kotun da aka shirya gudanarwa a wannan Litinin din daya ga watan Agusta ba.

Mai shekaru 67 a duniya Gbagbo na fuskantar tuhuma dangane da zargin hannun a cin zarafin dan Adam, yayin rikicin bayan zabe na 2010 zuwa 201, inda mijinta Laurent Gbagbo ya ki amincewa da kayen da ya sha. Shi ma mai gidan nata kana tsohon shugaban kasar ta Côte d’Ivoire Laurent Gbagbo dai, na fuskantar tuhuma kan cin zarafin dan Adam din a kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta kasa da kasa ICC.

You may also like